Yau ga Mutumin da aka daure fiye da sau dubu a duniya

Yau ga Mutumin da aka daure fiye da sau dubu a duniya

- Yayin da wasu ke tsoron su aikata laifi, ga wani nan ya aikata laifuffuka ya fi a kirga a duniya

- An kama wannan ta’aliki fiye da sau dubu a rayuwar sa

- Duk shi kadai, an daure shi sau kusan 1300

Yau ga Mutumin da aka daure fiye da sau dubu a duniya

Yayin da wasu ke tsoron su aikata laifi, ga wani nan ya aikata laifuffuka ya fi a kirga a duniya. Watakila ba ka taba jin wannan gogan mai suna Henry Earl ba? Wannan mutumin ya fi kowa shan kamu a duk duniya.

Henry Earl ko kuma kace masa James Brown ya shiga Tarihin duniya, inda ya zama wanda ya fi kowa shan dauri a duniya. Sau kusan 1300 Hukuma tana kama wannan mutumi a rayuwar sa. Ko ka taba jin wani namji a duniya irin sa?

KU KARANTA: Hukumar EFCC tayi wani wawan kamu

Yanzu haka James Brown ya kai shekaru 66 a duniya, ya kuma fara shiga gidan yari ne a shekarar 1970, watau kusan shekaru hamsin da suka wuce. A wancan lokaci Henry Earl yana dan matashi mai shekaru 20 rak a duniya da haihuwa. An dai saba kama Henry tun wancan lokacin da laifin maye a cikin Jama’a, daukar makami da dai sauran su.

Henry Earl mutumin Lexington ne, na Kentucky ta Amurka. Wannan mutumin masifaffen mashayin giya ne dai a duniya. James Brown dai ya zauna a gidan yari na kwanaki fiye da 6000 a rayuwar sa ta duniya. A shekarar 2003 yayi kaurin suna a duniya bayan Gidan CNN ta fito da shi. Watakila Har ma dai ya saba da gidan kaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel