Daliban Najeriya da ke Kasar Russia suna cikin wani hali

Daliban Najeriya da ke Kasar Russia suna cikin wani hali

Daliban Najeriya da ke Russia sun yi zanga-zanga a Ofishin jakadancin Kasar da ke Moscow

Daliban Kasar da ke karatu a can sun koka da yadda Gwamnatin Tarayya tayi watsi da su

Sun ce an fi shekara daya ba a biya su dan alawus din su ba

Daliban Najeriya da ke Kasar Russia suna cikin wani hali
Dalibai sunyi zanga-zanga

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa daruruwan Daliban Najeriya da ke Turai sun koka da yadda Gwamnatin Tarayya tayi watsi da su.

Daliban Najeriya da ke karatu a Kasar Russia sun yi zanga-zanga a Ofishin Jakadancin Kasar Najeriya da ke Babban Birnin Kasar ta Moscow.

Daliban sun yi wannan zanga-zanga ne saboda rashin biyan su dan albashin su, sun ce rabon da su samu kudin su an fi shekara daya.

KU KARANTA: ASUU tace Gwamnatin Shugaba Buhari tana wahalar da yan Kasa

An dai tura wadannan dalibai karatu ne ta wata yarjejeniyar Kasa-da-Kasa, a yarjejeniyar Kasar Russia za ta dauki nauyin kudin karatun daliban.

Sannan Najeriya ta dauki nauyin ciyar da daliban Kasar na ta da kuma lafiyar su inda ta ke biyar kowanne Dala dari biyar a kowane wata.

Sai dai yanzu shekara daya cur kenan Gwamnatin Tarayya ba ta biya wannan kudi ba, don haka ne Shugaban daliban Kasar da ke can, Faith Tosin ta jagoranci zanga-zanga zuwa Ofishin Jakadancin Kasar da ke Russia.

Wani Jami’in jakadanci Kasar da ke Russia ya kira daliban su rubuta takarda zuwa Ma’aikatar Kasar wajen Kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel