Dan Najeriya ya kafa tarihin tuka keke da daukan kwallo a kai

Dan Najeriya ya kafa tarihin tuka keke da daukan kwallo a kai

Wani dan Najeriya mazaunin kasar Cambodia mai suna Harrison Chinedu ya sake kafa tarihi a kundin tarihi na duniya.

Dan Najeriya ya kafa tarihin tuka keke da daukan kwallo a kai

Shida Chinedu ya kasance yana tuka keke zuwa tsawon zango, yayin dayake dauke da kwallo a kansa, a wannan karo Chinedu ya kwashe tsawon kilomita 103.6 yana tuki da kwallo a kansa.

KU KARANTA: Rikicin ýan Tasha: An jikkata jama'a da dama a jihar Legas

Dan Najeriya ya kafa tarihin tuka keke da daukan kwallo a kai

Ba wannan bane karo na farko da Chinedu ke shiga kundin tarihin Duniya domin a watan Maris na 2016 ma ya tuka keke dauke da kwallo a kai har tsawon kilomita 48.08 akan titin Ibadan zuwa Legas.

Dan Najeriya ya kafa tarihin tuka keke da daukan kwallo a kai

sai dai binciken da mu kayi a shafin yanar gizon kundin tarihin Duniyar (guinnessworldrecords.com) ya bayyana cewar ba’a riga an shigar da tarihin da Chinedu ya kafa ba a shafin.

Zaku iya bin kadin labaran mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

kalli bidiyon Chinedu a nan

Asali: Legit.ng

Online view pixel