Majalisar dattawa na kawowa Shugaba Buhari cikas

Majalisar dattawa na kawowa Shugaba Buhari cikas

- Da alamu majalisar dattawa ba za ta amince da kasafin kudin shekara mai zuwa ba

- Majalisar tace akwai gyara a takardun kasafin kudin da Shugaba Buhari ya kawo da kuma majalisar dattawa ta kasar tace sai an duba canjin Naira zuwa Dalar Amurka da sauran wasu abubuwa

Majalisar dattawa na kawowa Shugaba Buhari cikas
Shugaba Muhammadu Buhari

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Majalisar Dattawa ta Kasar nan ta fara nuna cewa fa ba za ta amince da kasafin kudin shekara mai zuwa da Shugaban Kasa ya fara turawa ba. Majalisar tace akwai gyare-gyare da ya kamata a cikin lissafin kasafin kudin Kasar.

Kwanaki ne dai Shugaban Kasa ya tura takardar da ke nuna yadda Gwamnati za ta kashe kudi a Kasar, sai dai Sanatocin Majalisar Dattawa sun ce abin fa da sake wani zama da suka yi Ranar Talata.

KU KARANTA: Ba za a rainawa Gwamnatin Tarayya wayau ba - Minista

Majalisar tace akwai abubuwan da ya kamata ayi la’akari da su kamar yawon gangar mai da za a hako a Rana, da kuma Darajar Naira da dala. Shugaba Buhari dai yana da aniyar kashe sama da Naira Tiriliyan shida, kusan dai Dala Biliyan $22.57 na Amurka.

Sai dai ba zai yiwu a kashe wannan kudi ba sai Majalisar Dattawa ta amince. Shekaran nan dai, haka aka yi ta fama, aka dauki dogon lokaci kafin a amince da kundin kasafin kudin Kasar.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

 

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel