Shirin Madadi don kawar da tsaffin jini a fim

Shirin Madadi don kawar da tsaffin jini a fim

- Masana’antar shirya finafinan Hausa Kannywood ta bude sabon shafin na ci gaban sana’ar da ta hanyar tsarin tantance sabbin ‘yan wasa

- An kira taron tantace ‘yan wasan da za su fito a fim din Madadi, masu sha’awa sun zo daga ciki da kuma wajen Kano domin a tantance su

Shirin Madadi don kawar da tsaffin jini a fim
Wasu daga cikin jaruman kannywood a lokacin taron
Shirin Madadi don kawar da tsaffin jini a fim
Jarumai mata ma ba a barsu a baya ba

A wani tsari na sake fasali da kuma samun sabbin jarumai a shirin finafinan Hausa, an gudarnar wani taron tantance masu sha’awar fitowa a fim din Madadi a Kano.

Na gundanar da wannan taron tantancewa ne a ranakun Lahadi 28 da kuma 29 ga watan Nuwamba a inda ya samu halaratar tsaffin jaruman da ke fitowa a finafinai, da sabbi, da kuma wadanda suke da sha’awar fitowa a finafinan hausa.

Tsohon Marubuci da ba da umarni Bala Anas, wanda ya jagoranci tantacewar, kuma mai ba da umarni a fim da Madadi ya ce, irin turuwar da jama’a suka yi na a tantance su, ya ba shi mamaki.

Kimanin mutane 168 ne suka nuna aniyarsu ta zuwa a tantance su, wasu ma daga Nijar, amma saboda dailili na matsi tattalin arzki shi ya sa wasu ba su zo ba, saboda kowa zai dauki nauyin kansa ne, amma mun samu jama’a daga Sokoto Kebbi da dan jami’a daga Zaria da yawansu ya kai kimanin 100.”

 Awwalu Zubairu wanda ya shirya shirin Madadi cewa ya ke yi, “kwalliya ta biya kudin sabulu hakan zai sa a samu sabbin jini wadanda za su fito a matsayin jarumai a shirin fim, kuma wadanda suka zo  tantance su domin shiga shirin madadi hakikiya nuna cewa muna da kwarraru masu basira da fasaha da aka yi watsi da su.”

Bashir Mudi da kuma Shehu Daneji tsaffin hannu a shirin fim na masu cewa, shirin fim sana’a ne, kuma shigo da jama’ar gari sana’ar zai sa a daina la’antarta, saboda ‘ya ‘yan wadanda ke suka su za su zama ganau da jiyau, ba da labarin gaskiyar lamari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel