Yau EFCC za ta shiga Kotu da Ibrahim Shema

Yau EFCC za ta shiga Kotu da Ibrahim Shema

– A yau Hukumar EFCC za ta shiga Kotu da Barista Ibrahim Shema

– Ana zargin Tsohon Gwamnan na Jihar Katsina da laifi da dama

– Tuni dai Jami’an tsaro na ta sintiri a Jihar

Yau EFCC za ta shiga Kotu da Ibrahim Shema
Yau EFCC za ta shiga Kotu da Ibrahim Shema

A yau ne dai za a gurfanar da Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema a gaban Babban Kotun Jihar da ke cikin Garin Katsina. An rahoto cewa Jami’an tsaro sun cika Jihar ko ta ina, wata majiyar mu ma ta nuna cewa har Gidan Tsohon Gwamnan yana zagaye da Jami’an MOPOL.

Tsohon Gwamnan Jihar dai yace wannan duk aikin Jam’iyyar APC ne. Tun da Gwamna Aminu Masari ya hau mulki, Hukumar EFCC da ICPC da sauran kwamiti sun shiga binciken Tsohon Gwamnan, sai dai Shema yace baa bin da yake tsoro don kuwa bai yi ba daidai ba.

KU KARANTA: Labaran Hausa da dumi-dumin su

Gwamna Aminu Masari dai yace Shema ya ji da kan sa da kuma abubuwan da ya aikata lokacin yana kujera, ya kuma daina ganin laifin sa. Mabiya bayan ‘Yan siyasan dai suna ta musayar baki a tsakanin su.

Kwanakin baya Hukumar EFCC su ka dura Gidan wani sirikin Tsohon Shugaban Kasa Goodluk Jonathan. Jaridar Premium Times tace an ga Jami’an tsaro dai sun zagaye Gidan da ke Unguwar Maitama ta masu kudi a Abuja.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel