• 370

    USD/NGN

Ana ta kama ‘Yan Boko Haram

Ana ta kama ‘Yan Boko Haram

– Jami’an tsaro suna cigaba da damke ‘Yan Boko Haram a cikin Kasar nan

– DSS tana samun nasara wajen kama masu satar mutane da sauran su

– Hukumar ta DSS ta sha alwashin kare rayukan mutane

Ana ta kama ‘Yan Boko Haram

Ana ta kama ‘Yan Boko Haram

Jami’an Tsaro na DSS suna cigaba da damke ‘Yan Boko Haram da sauran masu laifi a cikin Kasar. Hukumar tace tayi nasarar damke masu laifuffuka da dama a cikin Kasar; daga masu garkuwa da mutane zuwa ‘Yan ta’adda.

Wani Jami’in Hukumar mai suna Tony Opuiyo ya bayyana cewa Hukumar ta DSS ta kama wasu ‘Yan Boko Haram har guda 2 a Jihar Taraba. An dai damke ‘Yan ta’addan ne bayan sun tsere daga Garin Marte a Maiduguri. An kuma samu nasarar kama wani Babban Dan Boko Haram din a Okene cikin Jihar Kogi.

KU KARANTA: Ikon Allah: Gawa tayi layar zana

Kafin nan dai an kama wasu masu garkuwa da mutane a Nasarawan Jihar Kano da kuma wani a Karamar Hukumar Ningi da ke Bauchi. Tun ba yau ba dai Hukumar take damke masu garkuwa da mutane har a Yankin Neja Delta. Yanzu Hukumar ta damke ‘Yan Boko Haram kusan 13 a fadin Kasar.

Kwanki an kama wani Dan Boko Haram yana rike da Al-Qur’ani da kuma casbaha yana bara a cikin kasuwar Abuja. A baya kuma dai aka taba kama wani a Jihar Legas.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita da kuma Facebook

Related news

Daliban firamare nayi wa Gwamnan Taraba zanga-zanga

Daliban firamare nayi wa Gwamnan Taraba zanga-zanga

Mummunan rikici ya barke tsakanin Gwamna da ma'aikatansa
NAIJ.com
Mailfire view pixel