Shagalin haihuwa: Buhari ya ga Buhari

Shagalin haihuwa: Buhari ya ga Buhari

A jiya ne aka hangi shugaban kasa Muhammadu Buhari cike da farin ciki yayin da ya hadu da wani jariri da aka haifa a wani karamin asibitin daya je kaddamarwa a Abuja, wanda aka raɗa ma suna Muhammadu Buhari.

Shagalin haihuwa: Buhari ya ga Buhari

Shagalin haihuwa: Buhari ya ga Buhari

KU KARANTA:Wai! An sace gawa daga kabarinta a Afirka ta kudu

An haifi jariri Muhammadu Buhari ne a karamin asibitin shan maganin na matakin farko dake Kuchigoro a ranar 3 ga watan Janairu, kuma shine jariri na farko da aka fara haifa a wannan sabon asibiti.

Asibitin dai ya fara aiki ne tun a ranar 15 ga watan Disamba, sai dai a ranar Talata 10 ga watan Janairu ne shugaba Buhari ya kaddamar da asibitin.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewar shugaba Buhari ya kaddamar da aikin asibitin da aka gyara, wanda yana cikin manufofin gwamnatin tarayya na gyara kananan asibitocin shan magani a matakin farko guda dubu goma (10,000) da za’a fara nan bada dadewa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel