Mansa Musa: Hamshakin attajirin da yafi kowa arziki a tarihin duniya

Mansa Musa: Hamshakin attajirin da yafi kowa arziki a tarihin duniya

Alhaji Musa Keita shine mutumin da tarihi ya nuna cewar yafi kowa arziki a duniya, an fi sanin Musa Keita da lakabin Mansa Musa, ma’ana Sarki Musa.

Mansa Musa: Attajirin daya fi kowa arziki a tarihi duniya
Mansa Musa: Attajirin daya fi kowa arziki a tarihi duniya

Mansa musa shine Sarki na goma a jerin sarakunan masarautar Mali, kuma yana da arzikin da a yanzu darajarta ta haura dala biliyan 400 ($400bn).

KU KARANTA:Hukumar Soji ta gargadi jama’a kan sabon salon kai hare hare da Boko Haram ta sauya

Ba kamar yadda ake yayatawa ba, tun a shekarun 1300 ake yin mulkin sarauta a nahiyar Afirka, wannan ya sanya ya kamaci duk wani dan Afirka ya dinga gudanar da bincike don sanin sahihin tarihin sa, ba kawai abinda turawa ke fada musu ba.

Mansa Musa: Attajirin daya fi kowa arziki a tarihin duniya

A zamanin sa, Mansa Musa ya ci masarautu 24 da yaki, wadanda ya mamaye su da karfin mulkinsa kuma ya hade su a masarautar sa. Masana tarihi da dama sun bayyana shakkun kimanta arzikin da aka ce Mansa Musa ya mallaka, inda suke ganin ai babu wasu takamaiman alkalumma dake nuni ga yawan arzikin sa, a cewarsu, arzikin Mansa Musa ya wuce misali.

Don haka idan aka tambayeka ‘wanene attajirin daya fi arziki a tarihi?’ da fatan kasan amsar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel