Messi ya fara yin bakin jini a kasar sa ta Argentina

Messi ya fara yin bakin jini a kasar sa ta Argentina

- An lalata mutum-mutumin fitaccen dan wasan Argentina, Lionel Messi a birnin Buenos Aires.

- Wadanda suka yi aika-aikar sun raba mutum-mutumin gida biyu, inda aka cire kai da hannuwa.

Messi ya fara yin bakin jini a kasar sa ta Argentina

Messi ya fara yin bakin jini a kasar sa ta Argentina

A watan Yunin da ya wuce ne aka kaddamar da mutum-mutumin dan kwallon wanda aka kera da azurfa.

Ba a dai san dalilan da suka sa aka lalata mutum-mutumin ba, amma mahukunta sun ce sun fara gyara abubuwan da aka lalata.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar CAN ta yabawa Shugaba Buhari

An kuma kera mutum-mutumin ne a lokacin da Messi ya sanar da yin ritayar buga wa Argentina tamaula... daga baya ne ya sauya shawara bayan an yi ta rokonsa.

An kafa mutum-mutumin Messi a kan titin Paseo de la Gloria a wurin da ake ajiye fitattun 'yan wasan kasar da suka taka rawa ciki har da Gabriela Sabatini dan kwallon tennis da Manuel Ginobili mai wasan kwallon kwando.

Ku biyo mu a Facebook: https://web.facebook.com/naijcomhausa/

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel