2019: Ana neman wanda zai canji Buhari

2019: Ana neman wanda zai canji Buhari

– ‘Yan Najeriya sun fara kokawo game da halin da Najeriya ke tafiya

– Mutanen Arewa sun fara neman wani dan takara

– Da alamu dai Obasanjo yana goyon bayan Rabiu Musa Kwankwaso da Sule Lamido

2019: Ana neman wanda zai canji Buhari

2019: Ana neman wanda zai canji Buhari

Mutanen Najeriya sun fara kokawa da babbar murya a wannan Gwamnatin ta Shugaba Buhari. Don haka ma dai Mutanen Arewa har sun fara neman wanda zai canji Shugaba Muhammadu Buhari nan da zabe mai zuwa.

Kusan dai shekaru biyu kenan da kafuwar Gwamnatin Buhari, har kuwa tsohon Shugaban Kasa Cif Obasanjo ya fara shirin marawa wasu tsofaffin Gwamnonin Yankin baya. Majiyar mu daga NAIJ.com ta nuna cewa Obasanjo zai goyi bayan Sule Lamido ko kuma Rabi’u Kwankwaso.

KU KARANTA: Shugabannin Arewa sun gana a Kaduna

Da alamu dai Obasanjo ya fi karkata da tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido wanda har yanzu ya ki barin Jam’iyyar PDP bisa Rabi’u Kwankwaso, tsohon Gwamnan Kano, wanda ya sheka zuwa APC lokacin da ta kafu.

Sanata Dino Melaye mai wakiltar Yankin Yammacin Kogi a Majalisar Dattawa yace a zabe mai zuwa babu wanda zai kara zaben wani ‘tsohon kwano’, yace don kuwa yanzu lokaci ne na samari ba ‘yan shekara 70 ba.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Kaico: Sama da mutanen Najeriya 1,000 ke garkame a kurkukun wata kasa

Kaico: Sama da mutanen Najeriya 1,000 ke garkame a kurkukun wata kasa

Kaico: Sama da mutanen Najeriya 1,000 ke garkame a kurkukun wata kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel