Trump ya fadi dalilin takaitawa Musulmi shiga Amurka

Trump ya fadi dalilin takaitawa Musulmi shiga Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shirin rage yawan mutanen da ke shiga Amurka daga kasashen musulmi ya zama wajibi saboda yadda duniya ke cikin rikici.

Trump ya fadi dalilin takaitawa Musulmi shiga Amurka

Trump ya fadi dalilin takaitawa Musulmi shiga Amurka

Trump ya shaidawa kafar yada labaran ABC cewa ba yana nufin dukkanin musulmi zai haramtawa shiga Amurka ba illa ‘yan kasashen da ke fama da rikici.

KU KARANTA KUMA: APC ta sammaci Shehu Sani kan harin baki da ya kaiwa Buhari

Sai dai shugaban bai fadi kasashen da ya ke nufi ba, amma ya taba cewa kasashen Turai sun tabka babban kuskure musamman Jamus da ta amince ta karbi dubban ‘yan gudun hijira.

Rahotanni daga Amurka sun ce shugaba Donald Trump zai haramtawa mutanen Syria shiga kasar, sannan za a dakatar da bayar da biza ga mutanen kasashen Iraqi da Sudan da Somalia da Libya da Yemen.

An tambayi Trump ko ya damu da cewan wannan zai fusata Musulmai a fadin duniya.

“Fushi? Akwai fushi da yawa a yanzu. Ta yaya zaka samu wasu?” cewar sa.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda

NAIJ.com
Mailfire view pixel