366

USD/NGN

Kungiyar likitoci a Najeriya na fuskantar rashin yawan ma'aikata

Kungiyar likitoci a Najeriya na fuskantar rashin yawan ma'aikata

Likita daya kacal ne ke kula da kimani marasa lafiya 6,000 a Najeriya. Kungiyar na fuskantar rashin yawan ma'aikata.

Kungiyar likitoci

Likitocin Najeriya

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya, WHO ta ce kowani likita a Najeriya na kula da kimani marasa lafiya guda 6,000.

Farfesa Titus Ibekwe, shugaban sashen kunnen, hanci da makogwaro (ENT) ta Jami'ar Abuja, babban birnin tarayya ya bayyana wannan a ranar Laraba,25 ga watan Janairu.

Farfesa Ibekwe ya ce wannan gibin na da hadari matuka ga kiwon lafiya a kasar. Farfesa wanda shi ne kuma tsohon mataimakin shugaban Kungiyar likitocin (NMA) a Najeriya, ya bayyana cewa ma'aikata likita a Nigeria na fuskanta wata masala ta kula yawan marasa lafiya.

Farfesa ya na cewa mafi yawa cikin kayan aikin kiwon lafiya a wurare daban-daban a kasar suna bukatan kula da kuma maye gurbin su da kayan aiki na zamani.

KU KARANTA KUMA: Amurka za ta aika Dalibai Duniyar wata

Ya ce, a yanzu aka, kasar Najeriya ta na gurbi na 187th daga 191 a didigan kungiyar kiwon lafiya ta duniya, WHO a gurbin sauran kasashen.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya, WHO ta bayar da shawara cewa mafi karanci likita daya ya halarci marasa lafiya 600 amma wannan shawara ta samu wata salo a Najeriya a inda likita daya na kula da kimani marasa lafiya 6,000.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya zata ƙara ma ma’aikata albashi

A halin yanzu, likitoci a karkashin wata kungiyar NMA sun koka a kan igantace kaiyakin aiki a wurare a kasar, yayin da kuma suka yi tir da shugaba Muhammadu Buhari da kuma sauran jigon jami'an gwamnati domin neman kiwon lafiya a kasashen waje.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Related news
Dan shekara 10 ya labarta yadda ya zama gawurtaccen dan fashi da makami

Dan shekara 10 ya labarta yadda ya zama gawurtaccen dan fashi da makami

Dan shekara 10 ya labarta yadda ya zama gawurtaccen dan fashi da makami
NAIJ.com
Mailfire view pixel