Shugaban kasar Gambia ya koma gida (HOTUNA)

Shugaban kasar Gambia ya koma gida (HOTUNA)

Dan gudun hijira sabon shugaban kasa Adama Barrow ya koma gida bayan tsohon shugaban kasa Yahya Jammeh ya bar karagan mulki.

Shugaban kasar Gambia

Shugaban kasar Gambia Barrow ya dira a Banjul

Daruruwan al’ummar gambia na murnar dawowar sabon shugaban kasa, Adama Barrow, wanda ya yi hijira zuwa kasar senegal tun kafin a rantsar da shi a makon da ta gabata.

Sabon shugaban na sanye da fararren tufafi da kuma hula, Barrow ya sauka a Gambia ne cikin wata matakan tsaro da ya ke samu daga dakarun yammacin Afrika gaba daya.

Shugaban ya nemi dakarun su kasance a cikin Gambia na watanni shida.

Wadannan hotuna na nuna yarda jama’ar kasar suka tarbeshi , bayan dawowarsa daga gudun hijira a kasar Senegal.

Shugaban
Shugaban
Shugaban
Shugaban
Shugaban
Shugaban
Shugaban
Shugaban

Tawagar gwamnatinsa da manyan mambobin Jam’iyyarsa, na daga cikin wadanda suka tarbe shi bayan isowarsa tare da iyalansa.

Za a shirya wani sabon rantsarwa ga shugaban a nan gaba kadan a filin wasa, a Banju, babban birnin tarayya Gambia , wannan sanarwar ya fito ne daga kakakinsa Halifa Sallah.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar likitoci a Najeriya na fuskantar rashin yawan ma'aikata

Komawar shugaban zai bude wata sabon shafi a rayuwar al’ummar Gambia da suka shafe shekaru 22 karkashin mulkin tsohon shugaba Yahya Jammeh da ya sha kaye a zaben Disamban 2016.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel