Dalilai 3 da zasu jefa Najeriya cikin matsananciyar yunwa wannan shekarar (Karanta)

Dalilai 3 da zasu jefa Najeriya cikin matsananciyar yunwa wannan shekarar (Karanta)

Wata Kungiyar da take kula da yalwa da karancin abinci wato Famine Early Warning System FEWS NET a wata sakamakon bincike da tayi ta ce ta nuna cewa nan gaba kadan kasashe kamar Najeriya, Yemen,kudancin Sudan, Malawi da Mozambique za su yi fama da matsanancin yunwa.

Dalilai 3 da zasu jefa Najeriya cikin matsananciyar yunwa wannan shekarar (Karanta)

Dalilai 3 da zasu jefa Najeriya cikin matsananciyar yunwa wannan shekarar (Karanta)

Rahotan ya yi bayanin wasu dalilai 3 wanda sune dalialan da suke ganin zai sa fada wananan matsala ta yunwa;

1. Yawan rikici

Kamar yadda bincike ya nuna kasashen da aka ambata a sama sun yi fama da rikice rikice a shekarun baya da suka wuce wanda illar hakan ya rage had-hadan kasuwanci, koran mutane daga garruruwan su wanda hakan ya rage ayyukan noma da zaman lafiya.

2. Rashin ruwan sama

Rashin isasshen ruwan sama shima ya sa ana iya samun matsaloli musamman wanda ya shafi harkar noma wanda hakan zai iya kawo karancin abinci. Rahotan ta bada misalan kasashen da suke fama da karancin ruwa a shekarar bara kamar kasar Afrika. Tsakiyar kasar Asia ita ma ta sami karacin saukar kankara wato snow, wanda idan ya narke yake zama ruwa kuma manoma ke amfani dashi domin nomar rani.

3. Tabarbarewar tattalin arziki

A binciken da kungiyar ta yi, ta gano cewa matsaloli kamar rikici, faduwar darajan kudi da kuma rashin adana su ke sawa a fada irin wannan matsalar wanda illar hakan shine yake kawo tsadan abinci a kasashe kamar Yemen, kudancin Sudan da kuma sauran su.

Bayan haka rahotan ya nuna cewa kasar Najeriya musamman yankin arewa maso gabas sun fara fama da yunwa tun a shekarar 2016 domin ayukkan Boko Haram.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Dattijuwa ta samu warakar makanta bayan aikin agajin Soji na inganta lafiya a Ribas
NAIJ.com
Mailfire view pixel