An kama wasu miyagun ‘yan kuna bakin wake 3 a jihar Zamfara

An kama wasu miyagun ‘yan kuna bakin wake 3 a jihar Zamfara

Wasu daga cikin ‘yan Boko Haram 3 sun shiga hannun jami’an tsaro a jihar Zamfara.

Najeriya Army

Masarautar zurmi a jihar Zamfara ta mika wasu ‘yan ta’adda Boko Haram 3 da ake zargi da ta’addanci ga rundunar sojojin Najeriya.

Kanar Abdullahi Adamu wanda shine kwamanda ta rundunar 223 Light Tank Batallion a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara ya tabbatar da wannan labari ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Janairu 2017.

Jaridar News Agency ta Najeriya ta rahoto cewa jami’an ‘yan banga suka kama wadanna ‘yan ta’adda da ake zargin a yakin.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram ta sake sace mata 7 a Askira Uba

A yayin da Kanal Adamu ke nuna wasu makamai da aka tattara a hannun ‘yan Boko Haram, ya ce tuni an tura su zuwa babban officin rundunar sojoji a Kaduna saboda a yi masu tambaya.

Kanar ya gode wa masarautar zurmi da kuma jami’an ‘yan banga da kokarin cewa miyagun mutane ba su da mafaka a yakin.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Kaico: Sama da mutanen Najeriya 1,000 ke garkame a kurkukun wata kasa

Kaico: Sama da mutanen Najeriya 1,000 ke garkame a kurkukun wata kasa

Kaico: Sama da mutanen Najeriya 1,000 ke garkame a kurkukun wata kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel