Osinbajo ya maidawa Kungiyar CAN martani

Osinbajo ya maidawa Kungiyar CAN martani

– Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo ya mayar da martani ga Kungiyar CAN

– Kungiyar CAN ta zargi Osinbajo yayi magana game da rikicin da ke faruwa a wasu wurare na Kasar

– Osinbajo yace zai tsaya tsayin-daka wajen kare gaskiya da dokar Kasa

Osinbajo ya maidawa Kungiyar CAN martani

Osinbajo ya maidawa Kungiyar CAN martani

Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya sha alwashin kare gaskiya da yin adalci. Osinbajo ya fadi wannan ne ta bakin mai magana da yawun sa, Laolu Akande. Osinbajo yana mai mayar da martani ga Kungiyar CAN.

Kungiyar CAN ta Kiristoci ta nemi Mataimakin shugaban Kasar ya sa baki game da abubuwan da ke faruwa ga Fastocin Kasar, inda suke gani ana harin su. Osinbajo wanda shi karan kan sa Fasto ne yace kowa a Najeriya daya yake ko a gaban Ubangiji.

KU KARANTA: Buhari da Aisha Buhari a Landan

Osinbajo yace zai cigaba kamar yadda ya saba da kare gaskiya, yana mai tabbatar da cewa wadanda suka saba dokar Kasa za su gamu da hukuncin su. Osinbajo ya kara tabbatar da kokarin wannan Gwamnati na ganin an kawo karshen rikicin Kaduna da ire-iren su.

Kwanan nan, Fasto Johnson Sulaiman na cocin na Omega Fire ya ba Mabiyan sa umarnin kashe duk wani Makiyayi da aka gani kusa da Cocin sa. Faston yace a yanka masu wuya nan take, sai dai wadannan kalamai sun sa har Hukumar DSS ta nemi Faston domin su zauna.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Dattijuwa ta samu warakar makanta bayan aikin agajin Soji na inganta lafiya a Ribas
NAIJ.com
Mailfire view pixel