Karuwa ta shafa ma maza 500 cutar kanjamau a jihar Zamfara

Karuwa ta shafa ma maza 500 cutar kanjamau a jihar Zamfara

Wata karuwa da ba’a san ko wacece ba ta ci kafar kare bayan an zarge ta da shafa wa akalla maza 500 cutar kanjamau a jihar Zamfara. A cewar wata majiyar yan sanda, matar, wacce ta fito daga kudancin kasar, ta tsere daga jihar bayan asirinta ya tonu.

Karuwa ta shafa ma maza 500 cutar kanjamau a jihar Zamfara
Karuwa ta shafa ma maza 500 cutar kanjamau a jihar Zamfara

Yan Hisbah na jihar, sun sa manyar farauta a kan karuwar. An bayyana cewa ta koma Gusau, babban birnin jihar, wasu yan shekarun baya inda take neman makiyaya, kafin ta bude shagon karuwanci a dakin da take haya a hanyar Igbo Road.

A cewar rahotanni, matar ta shafa wa abokanan harkarta da dama cutar mai karya garkuwar jikin dan adam, wanda suka hada da wasu manyan mutane a jihar, yayinda harkar karuwancin ta ya dade a Gusau.

KU KARANTA KUMA: Fitacciyar marubuciya Buchi Emecheta ta mutu a Landan

An bayyana cewa an tona asirin ta ne bayan wani hatsaniya da ya shiga tsakaninta da wani abokin harkarta, wanda a take ya zarge ta da cutar kanjamau kuma cewa tana yada shi ga abokan harkan ta.

An bayyana cewa guduwa da tayi daga unguwar bayan fadan yasa mutane da dama sun yarda da zargin cewa tana yada cutar mai karya garkuwan jikin dan adam.

Har yanzu ba’a san inda ta koma ba. Wata majiya ta bayyana cewa likitoci sun daura wasu manyan mutane da ta shafa ma cutar a kan magani, yayinda sauran mutane ci gaba da samun kulawa a asibitoci daban daban a jihar.

Lokacin da aka kira, shugaban Hisbah na jihar, Dr. Atiku Balarabe Zawiyya, ya bayyana cewa kungiyarsa na sane da ci gaban da kuma tabbatar da cewan wacce ake zargin ta gudu don tsere ma mutanen sa da suka je kama ta a gidanta. Zawiyya yace kungiyar sa zasu ci gaba da yaki da rashin tarbiya a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel