Obama ya sa kafar wando daya da Trump

Obama ya sa kafar wando daya da Trump

- Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya caccaki Shugaba Donald Trump kan matakin da ya dauka na hana Musulmi 'yan wasu kasashe shiga kasar

- Sanarwar da mai magana da yawun Obama, Kevin Lewis, ya fitar ta ce tsohon shugaban ya ji dadin zanga-zangar da ake yi domin tilasta wa Trump ya janye matakin da ya dauka

Obama ya sa kafar wando daya da Trump

Obama ya sa kafar wando daya da Trump

Ya kara da cewa Mr Obama yana kyamar nunawa mutane wariya saboda addininsu.

A cewarsa, zanga-zangar da mutane ke yi ta nuna cewa Amurkawa ba za su bari a gurbata mulkin dimokradiyya ba.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da wasu kafafen watsa labaran Amurka suka ruwaito cewa wasu jakadun kasar a kasashen duniya na shirin caccakar Shugaba Donald Trump a kan takaita dokokin karbar bakin-haure.

Wani daftarin rahoton da jakadun za su fitar, wanda BBC ta gani, ya ambato su suna cewa hana Musulmi shiga kasar ba zai sa ta samu kwanciyar hankali ba.

Sai dai jami'an fadar White House sun ce ya kamata duk wanda ke kyamar wannan matakin ya yi abin da ya ga dama.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel