367

USD/NGN

Hukumar FRSC ta bada shawara a haramta sana’ar achaba a fadin kasa ga baki daya

Hukumar FRSC ta bada shawara a haramta sana’ar achaba a fadin kasa ga baki daya

- Hukumar tabbatar da tsaron hanyar mota wato FRSC tayi kiraga haram sana’ar achaba da babur a fadin kasa ga baki daya

- Game da cewar FRSC, sun bada wannan shawara ne domin rage haduran kan titi a fadin kasa

Hukumar FRSC ta bada shawara a haramta sana’ar achaba a fadin kasa ga baki daya

Hukumar FRSC ta bada shawara a haramta sana’ar achaba a fadin kasa ga baki daya

Hukumar tabbatar da tsaron hanyar mota wato FRSC tayi kiraga haram sana’ar achaba da babur a fadin kasa ga baki daya.

Shugaba hukumar ta FRSC, Boboye Oyeyemi, wanda ya bayar da wannan shawara ga sakataren gwamnatin tarayya,yace haramtawa zai rage hadura a hanyoyin Najeriya.

Game da cewar jaridar Punch, Boboye Oyeyemi yace masu babur sune asalin ummul haba’isin manyan haduran kan hanya a fadin kasa,saboda haka ya kamata a duba yadda za’a haramta wannan sana’a ga baki daya.

KU KARANTA: Takaitaccen labaran abubuwam da suka faru ranan Talata

Oyeyemi yace: “ Bisa ga wannan dubi da muke yi, zamu iya tabbatar da cewa Babura bai gushe zama matsala a manyan titunan Najeriya ba.

“Za’a iya samu sauki nan gaba, idan gwamnatocin jiha suka haramta amfani da shi a wajen sana’a.

“Saboda haka, sakataren gwamnatin tarayya ya duba kuma yayi kira ga gwamnatocin jiha su haramta aikin achaba.”

A bangare guda, Hukumar tabbatar da tsaron hanyar mota wato FRSC ya alanta jerin takardun da ya wajaba kowani direba ya kasance yanada shi ko kuma a kwace motarsa.

Takardun sune: Lasisin direba, lasisin mota, takardan cancantan hawa titi, takardan inshore, hujjan mallakan motar, takardan koya.

https://twitter.com/naijcomhausa

Related news
Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa kan hadin kan Najeriya

Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa kan hadin kan Najeriya

Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa
NAIJ.com
Mailfire view pixel