RIKICI: Wani mafarauci ya harbi mutane 3

RIKICI: Wani mafarauci ya harbi mutane 3

Jami’an tsaro ta cafke wani mafarauci wanda ya harbi iyalansa da kuma wani fasto

Wani mafarauci

A cewa wata rahoto, wani mafarauci Jerome Adoko ya shiga hannun jami’an tsaro bayan ya harbi matansa, surukuwarsa da kuma wani fasto.

Adoko wanda ya fito daga Iwewe-Ichama a karamar hukumar Okpokwu ta jihar Binuwai ya harbe matarsa har lahira uwargida Reginaa Adoko, yayin da surukuwarsa Esther Edogar da kuma wani fasto Eze Udoh na jiyya a wata asibiti.

A cewar jaridar Punch Metro, mafaraucin da matarsa suna gardama akan mallakar wani fuloti, a inda shi Jerome ke iƙirarin mallakar filin. Ko da yake Regina ta ce mallakar dukansu ne saboda tare suka saka kudi a lokacin sayen fulotin.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga sun hallaka mutane 5 a inda suka bude wa wata masallaci wuta

Ma’auratan sun manta da wannan al’amarin har wata rana Jeromi ya fuskanci matarsa da zargin dafa wata naman daji da ya kashe daga farauta ba tare da izininsa ba.

Kawai kafin a hankara sai Jerome ya kai wa matarsa hari, a nan sai duciya ta dibeshi ya fito da bindigar farautarsa ya harbi ita matan. Kuma ya jikkata fasto Udoh da kuma surukuwarsa Esther a yayin da suke kokarin shiga tsakani.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandar jihar Binuwai ASP Musa Yamu ya tabbatar da cewa a halin yanzu Jerome na tsare a babban oficin ‘yan sandar jihar.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel