Tarayyar kasashen Afrika ta amince da ficewa daga kotun duniya (Dalili)

Tarayyar kasashen Afrika ta amince da ficewa daga kotun duniya (Dalili)

- An kammala taron shugabanin kungiyar kasashen Afrika ta AU a birnin Addis Ababa na Habasha, in da shugabanin suka amince da shirin janyewa daga kotun duniya ta ICC saboda abin da suka kira rashin adalcin da ta ke yi wa shugabanin Afrika

- Kungiyar ta yi korafi kan matakan da kotun ta dauka kan shugabanin kasashen Sudan Omar Hassan al Bashir da kuma na Kenya Uhuru Kenyatta

Tarayyar kasashen Afrika ta amince da ficewa daga kotun duniya (Dalili)

Tarayyar kasashen Afrika ta amince da ficewa daga kotun duniya (Dalili)

Taron ya kuma amince da mayar da kasar Morocco a matsayin wakiliya da kuma shirin rage dogaro da tallafin da kasashen Afrika ke samu daga kasashen duniya.

Kazalika taron ya zabi Moussa Faki Mahamat, ministan harkokin wajen Chadi a matsayin sabon shugaban kungiyar ta AU, in da ya maye gurbin Nkosazana Dlamini Zuma bayan ya doke abokiyar takararsa Amina Mohamed, ministar harkokin wajen Kenya a fafatawar da suka yi a zagaye na karshe don neman babbar kujerar.

A wani labarin kuma, Dakarun sojin Yammacin Afirka da aka tura kasar Gambia ta ce ta gano makamai a gidan tsohon shugaban kasar, Yahaya Jammeh.

Kungiyar ECOWAS ta ce an gano makamai da harsasai ne a gidan Yahya Jammeh dake cikin kauyen Kanilai.

Mista Jammeh ya bar kasar kwanaki 10 da suka wuce bayan da ya sha kaye a zaben shugaban kasar da shugaba Adama Barrow ya yi nasara a watan Disambar bara.

Mista Barrow ya bukaci dakarun ECOWAS su zauna a kasar don tabbatar da kwanciyar hankali a lokacin da tsohon shugaban ya bar Gambia.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Wani Babban malami a jihar Kano ya kalubalanci masu sukar Kasar Sudiya akan kafa cibiyar tace Hadisai

NAIJ.com
Mailfire view pixel