Majalisa za ta binciki Mukaddashin shugaban kasa

Majalisa za ta binciki Mukaddashin shugaban kasa

– Majalisar Dattawa za ta binciki Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo

– Majalisar za ta gudanar da bincike a game da Gidan Mataimakin shugaban kasar

– Sanata Dino Melaye ne zai yi wannan aiki

Majalisa za ta binciki Mukaddashin shugaban kasa

Majalisa za ta binciki Mukaddashin shugaban kasa

Majalisar Dattawa za ta gudanar da wani bincike a game da gidan zaman Mataimakin shugaban kasa wanda shine Mukaddashin Shugaban kasa a yanzu haka. Majalisar na zargi an tafka badakala wajen gina gidan Mataimakin shugaban kasar.

Jaridar Punch tace da alamu dai Majalisar Dattawa za ta gudanar da wani bincike a game da ginin da ake yi na gidan mai girma Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a cikin Birnin-Tarayya Abuja.

KU KARANTA: Buhari ya ki tabbatar da nadin Alkalin Alkalai

Sanata Dino Melaye wanda shine shugaban kwamitin kula da Birnin Tarayya a Majalisar yace kudin da aka ware har Miliyan N250 na ginin gidan Osinbajo yayi yawa. Sanata Melaye ya kuma ce an tsula kudi wajen ginin gidan Shugabannin Majalisar Kasar.

Kwanan nan aka gano dai cewa an buga cuwa-cuwa wajen harkar gidajen Shugabannin Majalisar da Mataimakan su. Sai dai Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ya karyata hakan.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Senata Misau a kotu bisa zarginsa da yada karerayi kan Sifeta Janar Idris

Labari da duminsa: Sanata Misau ya gurfana gaban kotu bisa zargin da ya jefa kan Sifeta Janar na 'yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel