Buhari zai dawo da biyan tsagerun Neja Delta albashin N65,000 duk wata

Buhari zai dawo da biyan tsagerun Neja Delta albashin N65,000 duk wata

Gwamnatin Najeriya ta ce, nan gaba kadan za ta biya basukan da tsoffin 'yan tawayen Niger Delta ke bin ta daga cikin kudaden da ake biyan su, a karkashin yarjejeniyar ahuwar da suka kulla da gwamnati a shekarar 2009.

Buhari zai dawo da biyan tsagerun Neja Delta albashin N65,000 duk wata

Buhari zai dawo da biyan tsagerun Neja Delta albashin N65,000 duk wata

Ofishin kula da biyan tsoffin 'yan tawayen ya bukace su da su kara hakuri kadan domin gwamnati na shirin biyan su kudaden watannin baya da suka wuce.

Akalla kowanne mutum guda na karbar Naira dubu 65 a kowanne wata.

Dakatar da shirin a baya ya sanya matasan kaddamar da hare-hare kan bututun mai, abin da ya sa man da Najeriya ke fitarwa ya ragu daga ganguna kusan miliyan 2 zuwa ganguna dubu 700 a kowacce rana.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamanoni 17 na yankin Kudancin Najeriya sun gana a jihar Legas

Gwamanoni 17 na yankin Kudancin Najeriya sun gana a jihar Legas

Gwamanoni 17 na yankin Kudancin Najeriya sun gana a jihar Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel