Karuwa ta zama Minista a wata Kasa

Karuwa ta zama Minista a wata Kasa

– Wai a bar tuna-baya Inji Hausawa Mahaukaci ya zama Sarki

– A Kasar Zimbabwe wata mai-zaman kan ta ta zama Ministar yada labarai

– Ministar ta roki a bar tuna baya

Karuwa ta zama Minista a wata Kasa
Karuwa ta zama Minista a wata Kasa

Wata Minista a Kasar Zimbabwe ta nemi ‘Yan Kasar su bar tuna lokacin baya, Ministar dai ta taba zaman kan-ta a baya, tace amma yanzu ai komai ya wuce, kuma kyaun ta a dai bar tuna baya.

Minista Kampamba Mulenga ta yada labarai a Kasar Zimbabwe tace abin da za ayi la’akari da shi yanzu shine aikin ta a matsayin Ministan yada labarai. Ministar tace yanzu ta canza ta kuma ajiye wancan aiki a gefe.

KU KARANTA: Malamin Izala ya nemi a hana bara

Ministar tayi wannan magana ne inda ta ke nuna takaicin ta da wasu da ke kiran ta da sunan da aka san ta a da. Kampamba Mulenga ta cewa Mutanen Kasar yanzu ta canza ya kamata kuma al’umma su ba ta girman ta. Kafin ta zama Minista a Gwamnati dai kamar yadda Daily Post ta rahoto kowa ya san ta a matsayin mai zaman kan ta.

A farkon wannan Watan tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya gabatar da jawabi a gaban Majalisar Amurka inda aka gayyace sa domin yayi magana game da matsalolin Najeriya musamman rikicin addini da sauran su.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita Muna nan a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel