Barayin shanu 195 sun shiga hannu a Najeriya

Barayin shanu 195 sun shiga hannu a Najeriya

Rundunar `yan sandan jihar Niger da ke Najeriya, ta sanar da samun nasararori bayan sabunta kokarinta na kawo karshen masu satar dabbobi, sata da garkuwa da mutane, hadi da masu aikata sauran miyagun laifuka a jihar.

Barayin shanu 195 sun shiga hannu a Najeriya
Barayin shanu 195 sun shiga hannu a Najeriya

Kwamishinan `yan sandan jihar Zubairu Mu`azu ya sanar da hakan yayin zantawar da yayi da manema labarai a garin Minna.

Mu`azu ya ce sakamakon hadin gwiwar da rundunar `yan sandan ta yi da sauran hukumomin tsaro, sun samu nasarar kame barayin dabbobi 195 tare da kwato shanu 612 a fadin jihar.

Ya ce daga cikin barayin dabbobin da suka shiga hannu akwai 24 da aka dade ana nema ruwa a jallo.

Kwamishinan `yan sandan ya kara da cewa, jami:an tsaro sun ceto mutane 21 da aka sace, yayin sumamen da suka kaddamar kan wurare da suka kasance maboya ga bata gari a sassan jihar.

A halin yanzu `yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun lashi takobin murkushe miyagun da ke ta`asa a yankunan Allawa, Kukoki, Pandogari, Isau, Kaffinkoro, Sarkin-fawa, Shiroro, Mangoro, Lapai da kuma Gurara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel