Miji na ya sakeni saboda bani da kashin arziki inji wata zawara

Miji na ya sakeni saboda bani da kashin arziki inji wata zawara

- Wani magidanci mai shekaru 38 kuma mazaunin garin Mararaba dake jihar Nasarawa ya roki kotu da ta raba shi da matarsa Mufliat saboda zargin da yake mata cewa mai farar kafa ce

- Yace shekaru uku Kenan yana fama da matsaloli wanda ya tabbatar masa cewa itace sanadiyyar fadawarsa wadannan matsaloli

Miji na ya sakeni saboda bani da kashin arziki inji wata zawara
Miji na ya sakeni saboda bani da kashin arziki inji wata zawara

Ya fada wa kotun cewa lokacin da ya je neman mafita akan matsalolin da ya ke fama da shi malaminsa wanda shine limamin masallacin garin Karu ya fada masa cewa matarsa ce dalilin fadawa matsalolin da yake ta fama da shi a rayuwarsa.

Mijin Mufliat, Lukuman ya tabbatar wa kotun cewa malaminsa ya fada masa cewa matarsa ta na da aljanu wanda ya kamata a fitar mata dasu.

Bayan haka sai ya yanke shawaran cewa matarsa ta je ta zauna da mahaifiyarsa a kauyensu ‘Ijebu Ode’ har sai bayan an fitar mata da aljanun kafin ta dawo.

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kai hari a Maiduguri

Kafin hakan ya faru sai mahaifin Mufliat ya turo masa ‘yan daba domin su hana hakan faruwa.

Ya ce a yanzu haka ya kasa zanan cikin gidansa wanda ya gina a shekarar 2016 saboda rashin samun kawanciyar hankali.

Muflait ta ce malamin maigidanta da yake bashi shawarwari ba malamin kirki bane boka ne domin sai da ya sa su suka cire suturansu da takalmansu kafin su ganshi ko a wancan lokacin.

Ta yi bayanin cewa ba za ta zama dalilin matsalolin da mijinta ya shiga ba domin bayan aurensu ne arzikinsa ya bunkasa in da har ya mallaki motar kansa sannan ya gina gidan kansa kuma kasuwancinsa suka bunkasa.

Ta kuma zargi mijinta da hada hannu da ‘yan fashi inda su ka sace mata kayan shago da kuma wadansu kayayyakinta dake gida.

Lukuman ya roki kotu da ta bashi daman sakin matarsa domin zama shi da ita ya ishe shi.

Alkalin kotun Ibrahim Shekarau ya daga shari’ar zuwa 21 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel