A shirye na ke na hakura da shugabancin PDP saboda wannan dalili - Ali Modu Sheriff

A shirye na ke na hakura da shugabancin PDP saboda wannan dalili - Ali Modu Sheriff

-Ai Modu Sharif wanda Kotu ta tabbatarwa da shugabancin PDP ya ce a shirye ya ke da ajiye mukamin idan har hakan zai kawo ci gaban jam'iyyar.

-Tabbataccen shugaban ya kuma ce zai yi maganin Fayose da Wike saboda shige makadi da rawa da suke yi

A shirye na ke na hakura da shugabancin PDP saboda wannan dalili - Ali Modu Sheriff
A shirye na ke na hakura da shugabancin PDP saboda wannan dalili - Ali Modu Sheriff

Ali Modu Sheriff da ya yi nasara game da turka-turkar shugabancin jam'iyyyar PDP ya yi wani jawabi mai kaduwa bayan rikicin da ya dade yana faruwa.

Sanata Ali Modu Sheriff da bayyana hukuncin da kotun daukaka kara ta Fatakwal na ranar Juma'a 17 ga watan Fabrairu ta yi, a matsayin nasara ga jam'iyyar, ya kuma ce yana iya hakura da shugabancin.

Shariff ya ce bukatar jam'iyyar na gaba da zamansa shugaba, sannan ya ce, "A shirye na ke na hakura da matsayin don jam'iyyar ta kai a gaci."

A hirarsa da 'yan jaridu Sharif ya kuma ce,

"Na tuntubi wasu shugabannin jam'iyyar ta mu don tsara yadda za mu gudanar da babban taronmu na kasa don magance rabuwar kai da rikicin shugabanci."

Haka kuma, biyo bayan nasararsa, sabon tabbataccen shugaban na PDP ya yi alkawarin hukunta gwamnan jahar Rivers Nyesom Wike da takwaransa na jihar Ekiti Ayo Fayose.

Sheriff ya yi wannan jawabi ne ranar Juma'a 17 ga watan Fabrairu bayan kotun daukaka kara a Fatakwal ta mayar da shi halattacen shugaban jam'iyyar PDP.

Tsohon gwamnan na jihar Borno ya yi alkawarin gyarawa jam'iyyar zama yana mai cewa "ta yadda nan gaba mutane irinsu Wike da Fayose ba za su sake samun damar mike kafa a jam'iyyarmu ba."

A ranar Juma'a 17 ga watan Fabrairu shekarar 2017 ne, Kotun da ke zamanta a Fatakawal jihar Rivers ta bayyana sakamakon taron jam'iyyar da aka gabatar a Fatakwal ranar 21 ga watan Mayu a matsayin haramtacce, a rahoton jaridar Tribune.

Alkalai guda uku da ke sauraron shari'ar sun yi ittifaki cewa Ali Modu Shariff shi ne halattacen shugaban jam'iyyar.

Wannan hukuncin ya kawo karshen rikicin shugabancin da ke addabar babbar jam'iyyar adawar, sakamakon bagarorin biyu na Ahmed Makarfi da Ali Modu Sheriff kowa na ikirarin shi ne halastaccen shugaba.

Bangaren Ahmad Makarfi sun yi alkawarin daukaka kara zuwa kotun koli.

Ga wani hoton bidiyo na zanga-zangar goyon bayan shugaban Buhari da aka yi kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel