Farfesa Kperogi yayi kaca-kaca da gwamnatin Buhari

Farfesa Kperogi yayi kaca-kaca da gwamnatin Buhari

Wani Farfesan Najeriya da ke zaune a kasar Amurka yayi kaca-kaca da gwamnatin shugaba Buhari inda yace ba ta da aiki sai karyar banza da yaudarar ‘yan kasa.

Farfesa Kperogi yayi kaca-kaca da gwamnatin Buhari

Farfesa Kperogi yayi kaca-kaca da gwamnatin Buhari

Farfesa Farouk Kperogi wani Malamin harshen Turanci a wata Jami’ar Amurka ya soki gwamnatin shugaba Buhari wanda ya kira makaryaciyar banza. Farfesan yace ba abin da gwamnatin Buhari take yi illa sharara karyar banza da wofi.

Ba dai yau wannan Farfesan ya fara sukar gwamnatin Buhari ba, bayan kuwa a da can ya goyi bayan shugaba Muhammadu Buhari. Farfesan ya kawo misalan yadda gwamnatin ke karya da wasa da hankalin ‘yan kasar.

KU KARANTA: Masu shirin kawowa Buhari cikas a zabe mai zuwa

Farfesa Kperogi yayi kaca-kaca da gwamnatin Buhari

Farfesa Kperogi yayi kaca-kaca da gwamnatin Buhari

Farouk Kperogi yace bai taba ganin gwamnatin da ta saka furofaganda a gaba ba kamar gwamnatin Muhammadu Buhari. Kperogi yace an dauki ma’aikata na musamman domin ayi wannan aikin a yaren Hausa da Turanci. Farfesan yace masu yada karyar da Hausa ma sun fi muni inda ya kawo wani misalin sakon da aka ce shugaba Buhari ya aikowa ‘yan Najeriya.

Yanzu haka dai shugaba Buhari yana Landan inda yake hutawa. A farkon makon nan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello a wayar tarho yake fada masa cewa kwanan nan zai dawo ya cigaba daga inda ya tsaya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar zana jarabawar Post UTME

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar zana jarabawar Post UTME

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar da dalibai zasu zana jarabawar Post UTME
NAIJ.com
Mailfire view pixel