Boko Haram: Ana ta kai hari a kasar Kamaru

Boko Haram: Ana ta kai hari a kasar Kamaru

– Kungiyar Boko Haram suna ta kai hare-hare a kasar Kamaru

– An kai hare-hare har 3 sai dai ba a samu wani rashin rayuka ba

– Daya daga cikin maharar ne ya kashe kan sa

Boko Haram: Ana ta kai hari a kasar Kamaru

Boko Haram ta kai hari a kasar Kamaru

‘Yan Boko Haram suna ta kai hare-hare a kasar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya. A cikin ‘yan awowin nan dai an kai hare-hare har 3 a yankin Arewacin kasar ta Kamaru mai suna Magdeme da ke kusa da Najeriya.

Sai dai an dace babu wanda ya rasu a harin da aka kai face daya daga cikin masu kai harin. Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘Yan Najeriya ne suka tafi kai harin cikin dare a kasar inda kuma Rundunar Sojin kasar su ka fi karfin su.

KU KARANTA: Al-majiran Zakzaky 'yan ta'adda ne-Gwamnatin tarayya

Kwanan nan dai aka kashe wani Sojin kasar Kamaru a Jihar Bornon Najeriya. An rasa Sojin ne a Garin Kumshe wajen wani aikin hadin-gwiwa da Sojojin Najeriya. A makon nan ne Majalisar dinkin Duniya UN tace an dai kashe maciji ne ba a sare masa kai ba.

Rundunar Sojin Najeriya dai ta buga da ‘Yan Boko Haram a Garin Chikun-gudu kwanakin baya. Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya nemi a gama da ragowar ‘Yan Boko Haram din kafin damina ya karaso.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2
NAIJ.com
Mailfire view pixel