An rage ma Malamai 11 muƙami a jihar Kros Ribas, sun koma masu gadi

An rage ma Malamai 11 muƙami a jihar Kros Ribas, sun koma masu gadi

Hukumar Ilimin bai daya (SUBEB) ta jihar Kross Ribas ta rage ma wasu malaman makarantun Firamari su 11 matsayi inda ta mayar dasu bangaren masu gadi, a karamar hukumar Biase saboda rashin nuna shaidan kammala karatun.

An rage ma Malamai 11 muƙami a jihar Kros Ribas, sun koma masu gadi

Gwamna Ben Ayade na jihar Kros Ribas

Shugaban hukumar, Dakta Steven Odey ne ya bayyana haka bayan kammala aikin tantance malaman jihar da hukumar SUBEB tayi.

Odey yace “Baku da aiki a bangaren koyarwa tunda baku da takardun shaidan yin kowane irin karatu, idan ko haka ne ta yaya zaku iyar koyarwa? Idan kuna son zama malaman makaranta, kuje kuyi karatu.”

KU KARANTA:Daga cin Ayaba, wani yaro ya kamu da cutar ƙanjamau

Odey bai tsaya nan ba: “Daga yau mun mayar daku bangaren masu gadin makarantar, domin magance matsalolin tsaro da take fuskanta.”

An rage ma Malamai 11 muƙami a jihar Kros Ribas, sun koma masu gadi

Shugaba SUBEB da malamai

Shugaban SUBEB din ya jaddada ma sauran malaman da aka tantance dasu kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu ta hanyar yin amfani da duk kayayyakin aikin da hukumar ta samar a makarantun, don inganta Ilimi a kasar gaba daya.

Dayake amsa tambaya kan tsaikon da ake samu wajen biyan albashin malaman Firamari, Odey yace: “Ba SUBEB ke biyan albashinku ba, ma’aikatan dake kula da kananan hukumomi ne ke biyanku albashi, amma da zarar an bamu daman biyanku albashi, ba za’a sake samun matsalar nan ba.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2
NAIJ.com
Mailfire view pixel