Ya kamata a zabi mace a matsayin shugaban kasar Najeriya a 2019 – Inji Farfesa Madawaki

Ya kamata a zabi mace a matsayin shugaban kasar Najeriya a 2019 – Inji Farfesa Madawaki

- Matan jihar Sokoto sun shawarci ‘yan Najeriya da su zabi mace a matsayin shugaban kasa a zaben 2019.

- Farfesa A'ishatu Madawaki ta ce ya kamata a ba mata karin sarari a gwammnati.

- Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bukaci matan Najeriya da su shiga harkokin siyasa da kuma sauran ayyukan ci gaban kasa.

Ku zabi mace a matsayin shugaban kasan Najeriya – Inji Farfesa Madawaki

Ku zabi mace a matsayin shugaban kasan Najeriya – Inji Farfesa Madawaki

Matan jihar Sokoto a ranar Laraba, 8 ga watan Maris sun yi kira da babban murya ga ‘yan Najeriya da su zabi mace a matsayin shugaban kasan Najeriya a zabe mai zuwa na shekara 2019. Sun bayyana wannan magana a wani gangamin bikin ranar mata na duniya 2017 a Sokoto.

Farfesa ilimin halin dan adam, A'ishatu Madawaki ta yi wannan magana a madadin mata, ta ce ya kamata a ba wa mata dama don taimaka wajen ci gaban kasa.

Madawaki wanda kuma malaman koyarwa a jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto ta kara da cewa, ya kamata a ba mata karin sarari a gwammnati.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Farfesa Yemi Osinbajo murnar cika shekaru 60

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal wanda sakataren gwamnatin jihar ya wakilta, Farfesa Bashir Garba, ya bayyana cewa gwamnati yafi fifita mata, yara da kuma marasa galihu a jihar.

Tambuwal ya yi kira ga matan Najeriya da su shiga harkokin siyasa da kuma sauran ayyukan ci gaban kasa.

Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta fara wannan bikin ranar mata ta duniya a shekara 1975

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar da dalibai zasu zana jarabawar Post UTME

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar da dalibai zasu zana jarabawar Post UTME

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar da dalibai zasu zana jarabawar Post UTME
NAIJ.com
Mailfire view pixel