An gano gidan da ake buga kudi a jihar Kebbi

An gano gidan da ake buga kudi a jihar Kebbi

A ranar Alhamis ne hukumar EFCC ta kai karan wasu magidanta 4 kan zarginsu da laifuka 4 wanda ya hada da bugawa da siyar da jabun kudi.

An gano gidan da ake buga kudi a jihar Kebbi
An gano gidan da ake buga kudi a jihar Kebbi

Rundunar ‘Civil Defence Corps’ ta kama Usman Ahmed, Isiyaku Mohammed, Mohammed Badadi, da Rilwanu Abdullahi da tsabar jabun kudaden daya kai naira 583,000 a garin Birnin Kebbi wanda daga baya aka mika su ga hukumar EFCC domin cigaba da bincike akansu.

Bayan da aka gama karanta musu laifukansu sun amince da laifukan da aka zargesu dashi sannan shi kuma lauyan da ya shigar da karan N U Ukoha ya yi kira ga kotun da ta hukunta su kamar yadda doka jihar ta tanada.

Lauyan da ke kare masu laifi S B Ka’oje ya roki alfarman kotun da ta yafe musu domin wannan shine karo na farko da suka aikata irin wannan laifi.

Ya kara da cewa masu laifin magidanta ne da iyalai kuma suna da mutanen da suke karkashinsu bayan haka.

Alkali Amobeda ya yanke wa kowane dayansu hukuncin zaman wakafi na shekaru 5 bisa ga laifin da suka aikata sannan hukuncin ya fara daga ranar da aka kama su ne.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel