Dandalin Kannywood: Soyayyar Rahma Sadau da Messi da kuma Neymar

Dandalin Kannywood: Soyayyar Rahma Sadau da Messi da kuma Neymar

- Fitacciyar 'yar finafin Hausa ta Kannywood Rahma Sadau ita masoyiyar 'yan wasan kwallon kafa ce

- Hakan ya bayyana ne a shafinta na dandalin sada zumunta da muhawara na Instagram a inda ta lika hotunan Messi da Neymar fitattun 'yan kungiyar Barcelona

Dandalin Kannywood: Soyayyar Rahma Sadau da Messi da kuma Neymar
Dandalin Kannywood: Soyayyar Rahma Sadau da Messi da kuma Neymar

Daga dukkan alamu da akwai wata soyayya mai karfi tsakanin fitacciyar 'yar finafinan Hausa ta Kannywood Rahma Sadau da taurarin kwallon kafa Messi da kuma Neymar na kungiyar Barcelona.

Hakan ya bayyana ne a shafinta na dandalin sada zumunta da muhawara na Instagram a inda ta lika hotunan Messi da Neymar fitattun 'yan kungiyar Barcelona a lokacin da suke murnar cin kwallo.

Dandalin Kannywood: Soyayyar Rahma Sadau da Messi da kuma Neymar
Messi da Neymar na kungiyar Barcelona

Sai dai a sakon na ta, jarumar ba ta banbance barcin makaho ba, ma'ana, ko soyayyarta ga kungiyar kwallon kafan ce ko kuma ta fitattun 'yan wasan ne biyu.

A karawar da aka yi ta baya-bayan nan kungiyar Barcelona ta lallasa ta PSG da ci 6 da 1 a camp Nou, bayan ta sha kashi da ci 4 da nema a karawar farko.

Rahama Sadau ba ita kadai ce ba a cikin 'yan finafinan Hausa da suke marawa kungiyar Barcelona baya tare da nuna matukar sha'awarsu ga taurarin kwallon kafa ba.

Jarumi kuma matashi Muhammad Bello Muhammad da aka fi sani General PMB na garin Jos, saboda kaunarsa ga kungiyar Barcelona har rana aka ware a bikinsa a inda aka yi shiga ta musamman ta kungiyar.

Ga zanga-zangar goyon bayan Buhari da aka yi a kwankin baya

Ku kalli ra'ayoyin mutane kan aure

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel