An damke fasto yana sata Komfuta kiran Apple

An damke fasto yana sata Komfuta kiran Apple

- An damke wani fasto a jihar Legas yana satan Kamfuta da wasu abubuwa

- Anyi ram da shi kuma an kwace abubuwa da dama a hannunsa

Abin kunya: An damke fasto yana sata Komfuta kiran Apple (Hoto)

Abin kunya: An damke fasto yana sata Komfuta kiran Apple (Hoto)

Wani marubucin kafar ra’ayi da sada zumunta ta Fezbuk, Uju Patricia, tace jami’ an yan sanda RSS na jihar Legas, sun damke wani babban fasto mai suna, Ikemefuna Aje.

Ikemefuna Aje ya amince da cewa ya aikata wannan laifi lokacin wata taro da aka shirya a Otal dake Ikeja, Jihar Legas.

KU KARANTA: An kashe fulani makiyaya a jihar Kaduna

Wata na’urar CCTV ne ta daukeshi yayinda yake halin beran. Ya sace MacBook Apple 5, HP 1, da kuma wasu abubuwa, wadanda ya kai shagunan sayar da Komfuta da wuri domin sayar da su.

Ya sayar da kayayyakin ga wani Saliu Ibrahim kudi, N1, 110, 000.

Amma da ta tashi, jami’an yan sanda sunyi ram da shi a wani gida mai lamba No 5 Tony Street, Ejigbo, Lagos inda ya shirya taron addu’a da wa’azi.

Bayan an damke shi, jami’an tsaro sun je gidansa inda suka ga wata mota Toyota Runner, Komfuta Inox, Mukulli mai bude komai, jakukunnan komfuta, da kudi N700,000.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2
NAIJ.com
Mailfire view pixel