Malami ya makantar da daliba da bulala saboda ta yi lattin zuwa makaranta (HOTO)

Malami ya makantar da daliba da bulala saboda ta yi lattin zuwa makaranta (HOTO)

Wata dalibar makaranta mai suna, Raliya Suleiman, ta rasa idonta na dama bayan daya daga cikin malamanta ya doke ta da bulala a kan ido.

Malami ya makantar da daliba da bulala saboda ta yi lattin zuwa makaranta (HOTO)

Raliya Suleiman

Raliya ta kasance dalibar makarantar karamar sakandare na gwamnati dake Kachai, an rahoto cewa wani malami a makarantar, Moses Aura ne ya zane ta saboda tayi lattin zuwa makaranta a ranar Alhamis, 23 ga watan Fabrairu, 2017.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa sakamakon dukar da malamin yayi mata, bulala ya sami dalibar a idon ta na dama, wannan ne yayi ma idon lahani na din-din-din. A halin da ake ciki, kawun Raliya, Sani Abubakar ya tabbatar da al’amarin.

KU KARANTA KUMA: An ceto ma’auratan Abuja da aka yi garkuwa da su (HOTUNA)

Ya ce: “A wannan ranar, 23 ga watan Fabrairu, 2017 Raliya tayi lattin zuwa makaranta sai malamin, Moses Aura ya bukaci ita da sauran dalibai da su tsuguna su jira shi. Lokacin da ya dawo, sai ya fara dukan ta sannan bulalan ya same ta a idon ta na dama. A take aka garzaya da ita zuwa asibitin ido, Kaduna, amma abun bakin ciki, sun ce ruwan idon ya tsiyaye kuma babu abunda zasu iya yi don dawo da idon.”

Source: Hausa.naij.com

Related news
Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar da dalibai zasu zana jarabawar Post UTME

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar da dalibai zasu zana jarabawar Post UTME

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar da dalibai zasu zana jarabawar Post UTME
NAIJ.com
Mailfire view pixel