Shugaba Buhari yayi maganansa na farko bayan dawowa bakin aiki

Shugaba Buhari yayi maganansa na farko bayan dawowa bakin aiki

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar Birtaniya bayan kwanaki 51 da yayi na jinya a ranan Juma’a, 10 ga watan Maris.

Ina farin cikin dawowa aiki – Buhari yayi maganansa na farko bayan dawowa ofis

Ina farin cikin dawowa aiki – Buhari yayi maganansa na farko bayan dawowa ofis

A lokacin da ya dawo, ya bayyana cewa ya dawo ranan Juma’a ne saboda Farfesa Yemi Osinbajo ya cigaba da aiki har karshen mako a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

A yau Litinin, 13 ga watan Maris, ya rattaba hannu akan wata wasikar da ya aikawa majalisan dattawa na bayanin cewa lallai fay a dawo aiki.

KU KARANTA: Gwamnati ta kulle wata makaranta a jihar Bauchi

Daga baya kuma, shugaban kasan yayi dan jawabi a shafin ra’ayi da sada zumuntarsa na Fezbuk cewa yana farin cikin dawowa aiki.

Yace: “ Ina farin cikin dawowa aiki. Kamar yadda nayi bayani da na dawo ranan Juma’a, hanya mafi kyau da yakamata sun biyaku akan goyon bayanku shine cigaba da bauta muku domin cigaban Najeriya."

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Dan sintiri ya harbe kan shi har lahira domin gwajin laya

Dan sintiri ya harbe kan shi har lahira domin gwajin laya

Dan sintiri ya harbe kan shi har lahira domin gwajin laya
NAIJ.com
Mailfire view pixel