Shugaba Buhari ya koma Ofis bakin aiki

Shugaba Buhari ya koma Ofis bakin aiki

- Shugaba Buhari ya karbi ragamar mulki daga hannun Mataimakin Sa Farfesa Osinbajo

- Osinbajo ya gana da Buhari game da harkokin kasa a Ofishin sa

- Rabon Buhari da Ofis kusan watanni biyu kenan

Shugaba Buhari ya koma Ofis bakin aiki

Shugaba Buhari ya koma Ofis bakin aiki

A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi ragamar mulki daga hannun Mataimakin Sa Farfesa Osinbajo bayan ya dauko dogon lokaci ba ya nan. Rabon Shugaba Buhari da Ofis kusan watanni biyu kenan dai.

Shugaban kasar ya isa Ofis kimanin karfe 11:00 na safe inda aka hange sa tare da dogarai masu gadi. Shugaban kasar ya gana da shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnati watau Alhaji Abba Kyari.

KU KARANTA: Osinbajo ya mikawa Buhari mulki

Shugaba Buhari ya koma Ofis bakin aiki

Shugaba Buhari ya koma Ofis bakin aiki

Sannan shugaban kasar ya gana da Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo na dogon lokaci kusan sama da awa guda inda suka yi magana game da Yankin Gabas ta tsakiya, tattalin arziki da kuma kasafin kudi da sauran sha’anin kasa.

Majiya daga Jaridar Daily Trust tace an yi fareti a fadar shugaban kasar a safiyar yau kamar yadda aka saba kowace Ranar Litinin dai ana canza Sojoji masu fareti a fadar gwamnatin. Ranar Juma’a shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar Ingila inda yayi doguwar jinya na sama da watanni biyu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2
NAIJ.com
Mailfire view pixel