• 363

    USD/NGN

Dan wasa Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi

Dan wasa Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi

– Babban dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya bar tarihi a Duniya

– Duk kasar Spain babu dan wasan da ya kai Ronaldo zura kwallaye ta kai

– Haka kuma Ronaldo ya fi kowa jefa kwallaye a Filin Santiago Bernabeau

Dan wasa Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi

Dan wasa Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi

Zakaran Duniya Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi a Duniya inda ya zama Dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a raga da kai. A karshen wannan makon ne Ronaldo ya kara jefa kwallo da kai a wasan su da Real Betis.

Yanzu haka Ronaldo yana da kwallaye 46 da ya ci da kai tun zuwan sa kasar Spain. Duk kasar dai ba a taba samun wanda ya ci irin wannan kwallaye a tarihi ba. Dan wasa Aritz Aduriz ne dama can ya fi kowa inda ya ke da kwallaye 45.

KU KARANTA: Za a kara tsakanin Man Utd da Chelsea

Dan wasa Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi a Spain

Haka kuma Ronaldo ne Dan wasan da ya fi kowa kwallaye a gida watau filin Santiago Bernabeau. Cristiano Ronaldo ya buge tsohon Dan wasan Kungiyar Santillana mai kwallaye 209 a filin wasan.

Yanzu haka dai Real Madrid tayi gaba a Gasar La-liga bayan ta doke Real Betis a Ranar Lahadi. Sergio Ramos ne ya ci kwallon karshen a wasan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Related news

Gwamnan jihar Borno ya umarnin dauka matasa 300 aiki

Gwamnan jihar Borno ya umarnin dauka matasa 300 aiki

Gwamnatin jihar Borno na shirin dauka ma'aikata masu digiri 300 aiki
NAIJ.com
Mailfire view pixel