• 363

    USD/NGN

LABARI DA DUMI-DUMI: Buhari, Saraki da Dogara na cikin ganawar sirri

LABARI DA DUMI-DUMI: Buhari, Saraki da Dogara na cikin ganawar sirri

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin ganawa da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kuma kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ana gudanar da ganawar ne a cikin ofishin shugaban kasa Buhari.

Saraki da Dogara sun isa dakin taron ne da karfe 12 na rana.

An tuko su biyun ne zuwa gaban ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin motar Saraki na aiki.

Wannan shine karon farko da zasu gana da shugaban kasar bayan ya dawo gida Najeriya a ranar Juma’a, bayan dogon hutu da yayi a kasar Ingila.

A ranar Litinin ne dai shugaban kasa Buhari ya aika wasika ga majalisar dokoki inda ya sanar da yan Majalisar batun komawar sa bakin aiki.

Cikakken bayani zai biyo baya...

Related news

Gwamnan jihar Borno ya umarnin dauka matasa 300 aiki

Gwamnan jihar Borno ya umarnin dauka matasa 300 aiki

Gwamnatin jihar Borno na shirin dauka ma'aikata masu digiri 300 aiki
NAIJ.com
Mailfire view pixel