Rikicin PDP: Gwamna Dickson da IBB na cikin ganawar sirri

Rikicin PDP: Gwamna Dickson da IBB na cikin ganawar sirri

Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson da tsohon shugaban kasa a mulkin soja Ibrahim Babangida na cikin ganawar sirri a Minna, jihar Niger.

Rikicin PDP: Gwamna Dickson da IBB na cikin ganawar sirri

Majiyoyi sun ce shugabannin biyu sun hadu ne a ranar Laraba, 15 ga watan Maris, a garin tsohon shugaban kasar a mulkin soja.

Gwamnan jihar Bayelsa yayi burus da yan jarida a gurin ganawar sannan yay a bar gurin a take bayan sun gama ganawar.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya sun maida martani yayinda wani Bahaushe ya tsaya takarar zabe a jihar Ebonyi

Wata majiya da tayi magana cikin sirri tace an gudanar da ganawar na tsawon mintuna 60 a gidan tsohon shugaban kasar dake Hiltop a garin Minna, jihar Niger.

Ya ce Dickson ya gana da Babangida kadai a dakin tulawarsa na sirri da ya nisanta daga mataimakansa da sauran yan siyasa.

Majiyar ta ce babu mamaki su biyun sun tattauna ne kan al’amuran jam’iyyar PDP.

“Bayan sa’a daya, Gwamnan ya fito daga ganawar sannan bai bayyana komai ban a dalilin ziyarar amma maimakon haka ya shige motarsa ya tafi,” cewar majiyar.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar zana jarabawar Post UTME

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar zana jarabawar Post UTME

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar da dalibai zasu zana jarabawar Post UTME
NAIJ.com
Mailfire view pixel