Shugaba Buhari ya ba da umurni a rabawa jihohi Naira Biliyan 500

Shugaba Buhari ya ba da umurni a rabawa jihohi Naira Biliyan 500

- Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ba ministar kudi da gwamnan babban bankin kasar umurnin sakarwa jihohi naira biliyan 500 cikin gaggawa.

- Shugaban ya ce kudaden na cikin rarar da aka samo daga kungiyar Paris Club da ta mayarwa Najeriya saboda ta biya fiye da bashin da kungiyar ke binta.

Shugaba Buhari ya ba da umurni a rabawa jihohi Naira Biliyan 500

Shugaba Buhari ya ba da umurni a rabawa jihohi Naira Biliyan 500

To sai dai yayin da ake shirin raba masu kudaden akwai wasu sama da Naira biliyan uku da ake zargin wasu gwamnoni da rashin bin ka'ida da tsare-tsaren da aka ba su na yadda za su yi amfani da kason farko.

Sabanin haka sun yi abun da suka ga dama da kudaden ko da yake gwamnati ba ta bayyana sunayen jihohin da suka yi gaban kansu da kudin ba.

A yanzu shugaban na fatan za'a bi ka'ida a wannan karon, inda ya yi a garesu da su yi abin da ya kamata.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Rikici ya barke tsakanin wani Dalibi da ke karatu a A,B.U da Malaman sa

Rikici ya barke tsakanin wani Dalibi da ke karatu a A,B.U da Malaman sa

Rikici ya barke tsakanin wani Dalibi da ke karatun PhD a Jami'ar A.B.U da Malaman sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel