Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane 3 (Hotuna)

Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane 3 (Hotuna)

- Hukumar yan sanda na kasa, a ranan Juma’a tace ta damke masu garkuwa da mutane 3 a zariya, jihar Kaduna

- Hukumar tayi ram da su ne bayan sun je wani aikin yin garkuwa a ranan Laraba, 15 ga watan Maris

Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane 3 (Hotuna)
Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane 3 (Hotuna)

A ranan Juma’a, 17 ga watan Maris, hukumar yan sanda tace ta damke yan garkuwa da mutane a garin Zariya, jihar Kaduna. Kakakin hukumar yan sanda,Jimoh Moshood yace masu garkuwa da mutanen sune: Nuhu Fulani, 32; Yahaya Muhammed, 26 da Aisha Bature, 23.

Moshood yace: “Masu garkuwa da mutanen sun kasance kan jerin sunayen wadanda ake nema. Yayin bincike, sun tona asirinsu cewa sune suke gudanar da sace-sace da kuma garkuwa da mutane a babban titin Zariya zuwa Kaduna.”

KU KARANTA: Naira ta takara daraja

Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane 3 (Hotuna)
Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane 3 (Hotuna)

Kana yace yan barandan sunyi bayani ga masu binciken yan sanda wasu rawa da suka taka wajen wasu laifuka a jihar.

" Kana wasu mutane sun gane su. Amma ana gudanar da bincike akansu da kuma sauran yan kungiyan da suka arce,”

Daga cikin abubuwan aka kwace a hannunsu sune AK 47, karamin bindiga, harsasai da waya Samsung S6.

An kama bindiga AK 47a cikin bayin wata Aisha wacce itace matar shugaban yan fashin.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel