Darajar Naira zata kara dagawa - Babban bankin Najeriya

Darajar Naira zata kara dagawa - Babban bankin Najeriya

Babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) ya kara jaddadawa jama'ar kasa cewa tabbas darajar Naira fa zata kara yin sama a cikin satin nan mai kamawa.

Darajar Naira zata kara dagawa - Babban bankin Najeriya

Darajar Naira zata kara dagawa - Babban bankin Najeriya

Mai magana da yawun babban bankin Isaac Okorafor shine yayi wannan bayanin a cikin wata sanarwar da ya fitar ga manema labarai. Mr. Isaac ya kara da cewa hakan zai tabbata ne kuwa saboda babban bankin ya gama dukkan shirye-shirye don kara zuba daloli a bankunan kasar.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayya za duba yiwuwar soma biyan Naira dubu 50 a matsayin mafi karancin albashin aa'aikata.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Sanata Chris Ngige ya ce nan da dan wani lokaci shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amince da kafa wani kwamiti mai wakilai 29 domin tattaunawa da kungiyoyin kwadago don fitar da tsarin mafi karancin albashin ma’aikata a kasar nan. An tsammanin mafi karancin albashin shine naira dubu hamsin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Dalilin da ya sa ba za a tsige mahaifin shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ba

Dalilin da ya sa ba za a tsige mahaifin shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ba

Dalilin da ya sa ba za a tsige mahaifin Nnamdi Kanu ba
NAIJ.com
Mailfire view pixel