367

USD/NGN

Shekau ya yi barazanar ci gaba da kai hari a Maiduguri

Shekau ya yi barazanar ci gaba da kai hari a Maiduguri

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya sake fitowa a wani hoton bidiyo inda ya ke ikirarin daukar alhakin hare haren kunar bakin wake da aka kai a garin Maiduguri Jihar Borno.

Shekau ya yi barazanar ci gaba da kai hari a Maiduguri

Shekau ya yi barazanar ci gaba da kai hari a Maiduguri

A cikin sakon bidiyon, shekau ya ce sun gwabza fada da sojoji a kan iyakar kamaru tare da karyata ikirarin gwamnatin kasar da ta ce ta kashe mayakan shi 60 cafke wasu 20 da kuma kubutar da mutane sama da 5,000 a makwannin da suka gabata.

A hoton bidiyon na tsawon minti 27 , shugaban na Boko Haram ya ce yana nan garau tare da karyata ikirarin an raunana shi.

Sai dai kuma yanayinsa da babatunsa ba kamar yadda ya saba ba, a hoton bidiyon da ya fito tare mayakansa biyu a bayansa sun rufe fuska rike da makami.

Wannan ne karon farko da shekau ya fito tun fitowarsa a hoton bidiyo a watan Disemban bara lokacin da sojojin Najeriya suka ce sun kakkabe ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Related news
Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa

Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa

Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa
NAIJ.com
Mailfire view pixel