Ashe Dangote ya fi su Donald Trump kudi

Ashe Dangote ya fi su Donald Trump kudi

– Mai kudin Najeriya Alhaji Aliko Dangote ya fi shugaban kasar Amurka kudi

– Arzikin Dangote ya fi jimilar abin da Trump da Oprah suka mallaka

– Mujallar Forbes ta Duniya ta bayyana haka

Ashe Dangote ya fi su Donald Trump kudi

Ashe Dangote ya fi su Donald Trump kudi

Jaridar Forbes ta bayyana cewa arzikin mai kudin Najeriya da ma Afrika Alhaji Aliko Dangote ya fi abin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya mallaka. Trump dai kasurgumin attajiri ne tun tuni amma Dangote ya sha gaban sa nesa ba kusa ba.

Bari ma dai dukiyar Dangote ta fi ta Donald J Trump hada da na bakar ‘yar kasuwar nan Oprah Winfrey ta Amurka. Dukiyar Dangote a yanzu haka ta kai akalla Dala biliyan $11 wanda ya ribanya abin da Trump mai Dala biliyan 3.7 da Oprah mai Dala biliyan 3 suka mallaka.

KU KARANTA: Ka ji abin da aka kama wani Dan Najeriya yayi

Ashe Dangote ya fi su Donald Trump kudi

Ashe Dangote ya fi su Donald Trump kudi

Dangote dai ya taba shigowa cikin sahun mutane 25 da suka fi kowa arziki a Duniya shekaru 3 da suka wuce. Shekara 6 kenan dai har yanzu babu wanda ya kai Aliko Dangote dukiya a kaf Nahiyar Afrika.

Shi dai tsohon shugaban kasa Dr. Jonathan Goodluck yayi kira ga ‘yan siyasar kasar da su zama masu gaskiya a duk inda su ke. Jonathan ya kira masu rike da matsayi su dage wajen taimakawa talakawan su a ko da yaushe.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP magoya bayan Ali Modu Sheriff sun shilla zuwa APC

Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP magoya bayan Ali Modu Sheriff sun shilla zuwa APC

Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP magoya bayan Ali Modu Sheriff sun shilla zuwa APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel