Wani babban Lauya ya maka Sanatoci kotu saboda shugaban hukumar Kwastam

Wani babban Lauya ya maka Sanatoci kotu saboda shugaban hukumar Kwastam

Wani babban lauya mazaunin garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya Mohammad Ibrahim ya shigar da kara a wata babbar kotun tarayyar yana kalubalantar majalisar dattijai game da Hamid Ali.

Wani babban Lauya ya maka Sanatoci kotu saboda shugaban hukumar Kwastam

Wani babban Lauya ya maka Sanatoci kotu saboda shugaban hukumar Kwastam

Babban lauyan ya shigar da karar ne a kotun yana mai kalubalantar tilascin da majalisar dattijai ta sa wa shugaban Kwastam akan lallai dole sai ya bayyana a gaban ta a cikin kayan sarki.

KU KARANTA: Majalisar dattawa zata binciki Saraki da Melaye

A cikin karar da lauyan ya shigar, yana bukatar da Shugaban hukumar ta Kwastam watau Hamid Ali, shugabannin majalisoshin dattijai da ta wakillai da kuma ministan shari'ar na kasar da su bayyana a gaban kotun don suyi wa yan Najeriya karin bayani.

Kawo yanzu dai kotun bata sanar da ranar da zata fara sauraron karar dake a gaban ta ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Sabuwar rundunar sojoji ta 8 ta fara aiki gadan-gadan a jihar Sokoto

Sabuwar rundunar sojoji ta 8 ta fara aiki gadan-gadan a jihar Sokoto

Sabuwar rundunar sojoji ta 8 ta fara aiki gadan-gadan a jihar Sokoto
NAIJ.com
Mailfire view pixel