Za a buga tsakanin Real Madrid da Barcelona a watan Afirilu

Za a buga tsakanin Real Madrid da Barcelona a watan Afirilu

- Hukumar gudanar da gasar cin kofin La Liga ta Spaniya ta tsayar da ranar da za a kece raini tsakanin Real Madrid da Barcelona

- Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona ne a wasan mako na 33 a ranar 23 ga watan Afirilu a Santiago Bernabéu

Za a buga tsakanin Real Madrid da Barcelona a watan Afirilu

Za a buga tsakanin Real Madrid da Barcelona a watan Afirilu

A watan Disamba kungiyoyin biyu sun tashi wasa kunnen doki a Camp Nou, inda Luis Suarez ya fara cin kwallo daga baya Sergio Ramos ya farke daf da za a tashi.

KU KARANTA: Darajar Naira ta kara yin sama

Madrid, wadda take ta daya a kan teburin La Liga, na fatan lashe kofin bana, wanda rabon ta da shi tun 2012 Barcelona ce ta biyu da tazarar maki biyu a teburin na La Liga.

Wasan da ake yi masa lakabi da El Clasico shi ne na karshe da kociyan Barcelona, Luis Enrique, zai kara da Madrid, bayan da ya sanar cewar zai bar Barca a karshen kakar bana.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas

Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas

Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel