Toh fa: ABU za ta yi magana a kan Sanata Melaye a yau

Toh fa: ABU za ta yi magana a kan Sanata Melaye a yau

- Majalisar dattijai ta yanke shawarar gudanar da bincike kan zargin cewa sanata Dino Melaye bai kammala karatun digiri ba

- Jami’ar Ahmadu Bello ta ce za ta bayar da cikakken bayyani kan karatun Melaye a jami’ar

Toh fa: ABU za ta yi magana a kan sanata Melaye a yau

ABU za ta yi magana a kan sanata Melaye a yau

Majalisar dattijai a ranar Talata, 21 ga watan Maris ta yanke shawarar gudanar da bincike kan zargin cewa sanata Dino Melaye bai kammala karatun digiri a jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria ba.

Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai, Ali Ndume ya yi wannan kira a kan ya kamata Majalisar Dokoki ta kasa ta gudanar da bincike kan zargin cewa sanata Dino Melaye bai kammala karatun digiri na farko da yake ikirarin yi a jami’ar Ahmadu Bello ba.

Ndume a wurin taron wakilan a ranar Talata, 21 ga watan Maris ya ce, a baya dai majalisar ta bincike tsegumin wasu takardar shaidar wanda ta shafe 'yan majalisar dokoki, ya ce kuma ya kamata a bicike wannan zargin wanda ta shafe takardar shaidar Melaye.

Har ila yau, ABU ta ce za ta bayar da cikakken bayyani a ranar Laraba, 22 ga watan Maris kan karatun Melaye a jami’ar.

KU KARANTA KUMA: Dino Melaye ya caccaki Ali Ndume akan takardan makaranta

A zaman ta gudanar karkashin mataimakinta Ike Ekweremadu, majalisar dattawan ta mika batun binciken, ga kwamitinta na da’a, domin gudanar da bincike tare da gabatar da rahotonsa a cikin makwanni hudu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Dalilin da ya sa mu ke shirin karbo bashi Inji Gwamnatin Buhari

Dalilin da ya sa mu ke shirin karbo bashi Inji Gwamnatin Buhari

Dalilin da ya sa mu ke shirin karbo sabon bashi Inji Gwamnatin Buhari
NAIJ.com
Mailfire view pixel