Abu yayi kyau: Naira tayi wani mugun tashi

Abu yayi kyau: Naira tayi wani mugun tashi

Naira tayi wani mahaukacin fisga a cikin dan lokaci kankani daga jiya zuwa yau. Yanzu haka mun samu labari cewa Naira tayi wani mugun tsalle a kasuwa

Abu yayi kyau: Naira tayi wani mugun tashi

Buhari da Gwamnan CBN

Darajar Naira ta daga kwarai da gaske daga jiya zuwa yau. A jiya ne dai babban bankin kasar watau CBN yayi taro game da batun kudin kasar. Ba a yi sa’a 24 ba kenan sai ga shi an ga wani mugun canji.

A yanzu haka, bayanai da mu ke samu sun nuna cewa ana sayar da Dala guda a kusan N400. A jiya Talata Naira ta motsa a kan Dalar Amurka da Dalar EURO ta Kasashen Turai. An saida Dalar a kan N430 sai ga shi yanzu ta kara zazzagowa.

KU KARANTA: Tattalin arziki Najeriya ya fara yin daidai

A Birnin Tarayya Abuja dai yanzu kana ana saida Dala a kan N410 ko ma N405. A can Legas kuma Dalar na tashi a kan N415 ga wanda zai saya sannan kuma N410 ga mai saidawa. Ana kuma saida Dalar Pounds a kan N520.

Dama can babban bankin Najeriya CBN ta ce kashin Dala ya bushe a wannan makon don kuwa za ta cigaba da sakin miliyoyin daloli domin a biya bukatar jama’a. Masu canji dai sun ce hakan ya taimaka wajen gyara lamarin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Mun amince da shugabancin shugaba Buhari dari bisa dari

Mun amince da shugabancin shugaba Buhari dari bisa dari

Mun amince da shugabancin shugaba Buhari dari bisa dari
NAIJ.com
Mailfire view pixel